====== Yammaci ======
**Directed by** [[director/Yakubu Muhd]] \\ **Produced by** [[producer/Class Two Kano]] \\ **Starring** [[actor/Aminu Hudu]], [[actor/Sani Danja]], [[actor/Bashir Qaya]], [[actress/Saratu Gidado]], [[actress/Hajara Usman]] \\ **Released** [[:list_of_hausa_films?dataflt=year=ND|ND]] \\ **Language** Hausa \\ **Running time** ??:??
===== Overview =====
//From http://hausafilms.net/sharhin_fim.htm (in Hausa)//
DAGA IBRAHIM MUSA GIGINYU
**FIM:** Yammaci
**KAMFANI:** Class Two, Kano
**DARAKTA:** Yakubu Muhammad
**TAURARI:** Aminu Hudu, [[actor/Sani Danja]], Bashir Qaya, Saratu Gidado, Hajara Usman, Jamila Haruna, Rukayya Umar, Ummi Nuhu, Mansura Isah, Rahma Ahmad
KISHI, masu iya magana su ka ce, kumallon mata. Duk da haka jarumtakar ’ya mace ita ce k'warewar ta wajen iya sarrafa zuciyar ta a kan kishi, sau da yawa kishi kan sa mata aikata katob'arar da za ta kai su ga aikin da-na-sani. To amma idan aka yi dace mace ta iya daurewa ta sarrafa zuciyar ta, sai ka ga ta kai ga samun nasara. Fim d'in ‘Yammaci’ na iya zama izna ga mata masu zafin kishi a rayuwa.
Labarin ’yan mata biyu ne, k'awaye, wad'anda su ke da zafin kishi, su ka kuma tsinci kan su cikin kogin son mutum d'aya.
Labarin ya fara ne salon da ba kasafai ake ganin finafinan Hausa da irin shi ba. Fim d'in ya fara ne da wak'a (wadda Hassan da matar sa Zuhra ke rerawa) Bayan wak'ar ne labarin ya fara, inda aka nuno Ni’ima (Rukayya Umar) da Sa’adiyya (Rahma Ahmad) sun dawo daga London, inda su ka je hutu tare da Alhaji (Aminu Hudu) wanda kuma shi ne mahaifin Ni’ima, sannan kuma kawu ne ga Sa’adiyya.
Sun shigo sun tarar da iyayen su mata, wato Hajara Usman (mahaifiyar Ni’ima kuma matar Alhaji) da Jamila Haruna (mahaifiyar Sa'adiyya kuma k'anwar Alhaji). Ni’ima ta nuna rashin jin dad'in ta game da rashin samun damar halartar bikin babbar k'awar ta Zuhra (Ummi Nuhu) da aka yi a Kano.
Bayan Ni'ima ta huta sai ta d'auki waya ta buga wa Zuhra ta yi mata murna, har ta ce kada ta sake mijin ta ya kashe ta. Domin duk ran da ya yi mata kishiya, to kamar ya kashe ta ne. Zuhra ta nuna wannan maganar ta kishiya ai sai dai bayan ran ta.
Hassan ([[actor/Sani Danja]]) shi ne angon Zuhra. Saboda irin son da Zuhra ke yi masa, abin har ya wuce makad'i da rawa. Domin ko kyauta iyayen ta su ka yi mata ba ta murna da ita, matuk'ar dai ba ta hannun mijin ta ta biyo ba. Al’amarin kuwa ya na bak'anta wa mahaifiyar ta rai.
Wata rana sakatariyar Hassan (Mansura Isah) ta saka masa wata wasik'a ta soyayya a aljihun sa. Ganin wannan wasik'a da Zuhra ta yi ya sa ta sha shinkafar b'era wai don ta mutu ta huta da zafin kishin tunanin kishin da ta ke yi. Da k'yar aka samu likitoci su ka ceto ran ta.
Hassan ya nemi sakatariyar tasa da ta rubuta wa Zuhura takarda cewa wasa ta ke yi don ya samu ta hak'ura hankalin ta ya kwanta. Da k'yar ta yarda ta rubuta. Ba a dad'e da yin haka ba Hassan ya rasa aikin sa, rayuwa ta yi tsanani.
Rannan sai wani abokin sa (Ubale Wanke-wanke) ya ba shi shawarar da ya tafi Legas wurin wani abokin su da ya yi kud'i. Haka kuwa aka yi, cikin dare Hassan ya tsallake matar sa bayan ya rubuta mata wasik'ar cewa shi ya tafi, amma ta jira shi ya tafi Legas, ya je wajen abokin sa ne (Bashir K'aya).
A Legas, K'aya ya gabatar da shi ga ubangidan sa Alhaji (Aminu Hudu). Aka ba shi aiki, ya murmure ya samu daula. A na cikin haka ne Ni’ima ’yar Alhaji ta kamu da son Hassan.
Ala dole saboda gudun kada Alhaji ya k'wace dukiyar da ya samu, Hassan ya yarda ya amshi goron soyayyar da Ni’ima (Ruk'ayya) ta mik'o masa. Ya kuma yarda zai aure ta, amm duk a cikin rashin sanin cewa k'awar matar shi ce da ya baro a Kano.
Al’amurran biki dai su ka kankama, an sa rana har an fara raba katin gayyata, kwatsam sai Ni'ima ta ce za ta Kano. Hassan ya nuna rashin amincewar sa, amma dole ta sa ya hak'ura.
Ni’ima ta isa Kano, ta je har gidan Zuhra ta kai mata katin gayyata. Zuhura ta kama hanyar zuwa tashar mota sai aka yi mata waya, ta na cikin amsa wayar sai fim d'in ya k'are.
Ko Zuhra na had'uwa da mijin nata a Legas? Me zai faru idan ta gano cewa ashe mijin k'awar ta ne za ta aura?
SHARHI
Fim d'in ya yi kyau, sai dai ya na tattare da sark'ak'iya. Labarin ya sami jigo mai k'arfi. Kazalika, jerin jaruman sun dace da rawar da su ka taka. Tabbas a iya ba fim d'in tambarin “Da kyau.”
DARASI
Fim d'in ya na d'auke da darussa kamar haka:
Illar zafin kishi.
Illar rashin fad'in gaskiya.
Illar abokan banza.
KURAKURAI
Duk yadda al’amari ya kai ga tsaruwa, ba za a rasa ’yan kurakurai ba. Kurakuran da ke cikin ‘Yammaci’ sun had'a da sautin hayaniyar mutane a lokacin d'aukar shirin. (Aminu Hudu) ya d'an so ya wuce gona da iri, domin lokacin da aka kawo Hassan wurin sa ba a nuna matsalar da ke damun sa ba sai kuma Alhaji ya yi karaf ya kawo maslaha. Sannan ba a nuna dalilin da ya sa Hassan ya k'i fad'in ya na da aure ba.
A saurari kashi na biyu
===== Share this page =====