Leadership Article Archive (in Hausa)

Maryam ‘Malika’: Albasa Ba Ta Yi Halin Ruwa Ba?
By: Daga Nasir S. Gwangwazo, Abuja

Maryam ‘Malika

Na dade ban yi rubutu ba a kan lamarin da ya shafi sana’ar shirin fim. A takaice ma dai na yanke shawarar ba zan sake daukar alkalami, don rubuta wani abu a kan lamarin da ya shafi sana’ar shirin fim ba. To, amma saidai rikicin da ya taso a kwana-kwanan nan kan sabuwar jarumar nan, Maryam Muhammad, wacce a ke yiwa lakabi da Malika, wato sunan da ta ci a shahararren fim din da ta fito ciki kuma fim din da ya tallata ta ya ba ta suna da kima da daukakar da ba ta samu a gidan iyayenta ba, ya sanya na yanke shawarar dawowa bakin daga.
Ni da a tunanina na yanke shawarar daina rubutu don kashin kaina ne saboda ni ma na tsinci kaina dumu-dumu a cikin sana’ar, don a fahimtata zai fi dacewa na bar wadanda ba su cikinta kai-tsaye su bayar da labarinta, maimakon irina wadanda ke da ruwa da tsaki a ciki. Amma a yanzu ba domin komai na yanke shawarar sake tsoma alkalamin rubutu cikin tawada ba sai don cewa, idan mutum ya san gaskiya, amma ya yi shiru ya boye ta a lokacin da a ke bukatar ta, to lallai ya aikata zalunci, domin boye gaskiya ma zalunci ne mai girma.
A cikin mujallar Fim ta watan Maris 2012, wato daidai watan shekarar Hijira na Rabi’ul Thani 1433, an buga wata doguwar tattaunawa da Maryam, inda ta bayyana ‘nadamarta’ da shiga sana’ar shirin fim, sannan kuma ta yi tofin-Allah-tsine ga mafi yawan masu ruwa da tsaki a cikin sana’ar ta na mai danganta su da ‘bata’ ko kuma wadanda ba su tare da shiriya, duk da cewa, yayarta da su ka fito ciki daya wato tsohuwar jaruma nan Marigayiya Balaraba Muhammad ta rasu ne a cikin sana’ar a lokacin aurenta da dan fim, wato Shu’aibu Lawan, wanda a ke yiwa lakabi da Kumurci.

Amsar da Maryam ba ta bai wa mai karatu a hirar ba ita ce, shin Maryam ta na nufin yayarta Balaraba ta rasu ne ta na auren ‘batacce’ kuma a cikin bata ta koma ga Allah? A zahiri dai kowa ya san kyawawan halayen jarumar marigayiyar.

Haka nan Maryam ta kuma bayyana cewa, ba ta taba samun wani alheri ba a sanadiyyar fim. Sai dai kuma ba ta yiwa masu karatu bayanin cewa, mijin da za ta aura ta hadu da shi ne a sanadiyyar ’yan fim ba.

Bugu da kari, Maryam ta bayyana cewa, ko da ta ji wata ’yar gidansu a nan gaba za ta shiga sana’ar fim, za ta ba ta shawarar kada ta kuskura ta shiga, don ba abin arziki ba ne. To, amma ba ta gayawa duniya irin ranar da sana’ar ta fim din ta yiwa ’yan gidan nasu ba ta hanyar zama silar aurar da har guda biyu ba, ciki kuwa har da ita kanta mai ikirarin.

Haka nan ta bayyanawa duniya cewa, ba ta da kawa ’yar fim ko da guda daya kuma babu wacce za ta halarci bikinta daga cikin ’yan fim, amma saidai ba ta fadi dalili ko bakin halin da zai sa mutum ya yi tarayya ko mu’amula da daruruwa ko dubunnan mutane, amma a cikinsu a rasa ko da guda daya tak da za ki iya gayyata bikinki ba.

To, duk mu ajiye wadannan maganganu ko hasashe-hasashe na sama tunda dai Maryam ba ta nan wajen ballantana ta yi fashin baki; mu koma ga dalilan da su ka sanya jarumar ta yi wadancan kalamai kurum. A baya mun bayar da labarin yadda a ka kulle jarumar tare da saurayinta, wanda ta ke ikirarin za ta aura, a dalilin kin fitowa aikin cigaban Malika na hudu bayan an taru a Gusau babban birnin jihar Zamfara. Don haka ba sai mun yi doguwar bita dalla-dalla ba.

Shi dai fim din Malika, wanda Maryam ta na daga cikin jaruman da su ka jagoranci gabatar da shi, an shirya kashi na daya zuwa na uku ne da farko, sannan daga bisani a ka tasamma shirya kashi na hudu bayan da kashi na daya da na biyu su ka sami gagarumar nasara a kasuwa. Don haka a ka yanke shawarar shirya na hudun, don a sake shi tare da na uku.

Masu hikima sun san cewa, tarihi shi ne ma’aunin rayuwa kuma da shi a ke hasashen gaba. To, tarihi ya tabbatar da cewa, duk lokacin da a ka zo shirya cigaban shirin fim din da ya karbu, a kan samu matsala da wasu daga cikin ma’aikatan shirin, musamman jarumai wadanda a ka riga a ka ga fuskokinsu a cikin shirin. A na danganta hakan da hassadar da ke shiga cikin zukatan wasunsu, domin sun san cewa dole sai da su za a cigaba da shirin ba kamar sauran ma’aikata ba.

Idan dai za a iya tunawa, an sami gagarumar matsala tsakanin furodusan fim din Wasila, wato Yakubu Lere, da ita kanta jarumar, wato Wasila Isma’il lokacin da a ka zo shirya cigabansa. Lokacin da sulhu ya ki yiwuwa tsakaninsu, sai kashe ta a ka yi a cikin cigaban shirin dungurugum a ka kawo sabuwar jaruma.

Haka nan an sami matsala tsakanin kamfanin Square Media Arts da jarumar fim din Jidda, wato Jamila Nagudu, lokacin da a ka fara taso da maganar shirya cigaban fim din. Yanzu haka marubuta na can su na zaman dirshan din rubuta labarin cigaban shirin mai suna Dr. Rabo, ba tare da ita Jamilar ba.

Akwai misalai da yawa kan hakan, wadanda babu lokacin kawo su. To, don haka ba bakon abu ba ne a Kannywood don an sami matsala tsakanin wanda ya dauki nauyin shirya Malika, wato Sani Zamfara, da jarumar shirin. Amma abin mamaki ne jarumar ta fito ta gayawa duniya cewa, rigingimun da a ka samu tsakaninta da shi sun faru ne, domin kawai ya na son ta, kuma don ya ji za ta yi aure.

Ture maganar cewa, yayan Umar, wato shi wanda zai auri Maryam din, aboki ne a wajen Sani Zamfara, gefe guda, ka dubi lafazan da su ka fito daga bakinta, kamar yadda mujallar ta wallafa.

Maryam ta shaidawa mujallar cewa, Sani ya ba ta _200,000 a matsayin gudunmawar bikinta, to amma yayin da hirar ta dauki zafi sai ta sauya bakinta, inda ta ce, ya sanya ’yan sanda an kulle ta ne, domin ya na jin haushin za ta yi aure. To, wacce maganar a ciki mai karatu zai dauka? Ta farkon ko ta biyu? Sarki dai maganar farko ya ke dauka. Mutumin da ki ka ce ya ba ki gudunmawar biki, ya a ka yi kuma ya dawo ya kai ki kara a kan za ki yi aure?

Ta kafa hujja da cewa, Zamfara ya taba ba ta kyautar waya a lokacin da a ka sace tata a gidansa, a matsayin alama ta ya na son ta. Amma watakila Maryam ba ta san cewa, Sani Zamfara ya taba biyawa wasu ’yan fim kujerar Umrah da aikin Hajji ba. Haka nan watakila ba ta san cewa, ya taba bai wa wani marubuci kyautar waya mai tsadar gaske ba.

Mai yiwu kuma Maryam ba ta san cewa, Zamfara ya bayar da kyautar kwamfutar tafi-da-gidanka (labtop) ga wani darakta ba. Kana kuma ta yiwu ba ta san cewa, ya zuba zunzurutun kudinsa ya bugowa wasu furodusoshi da ’yan kasuwa finafinansu kyauta ba. Shin a kanta ya fara kyauta kenan?

Maryam ta kuma shaidawa mujallar cewa, lokacin da su ka je aikin Malika a Zamfara, shi Sani Zamfaran ya tambaye ta ina ne otel din da a ka sauke su, domin ya na so ya zo hira wajenta da daddare. Abin mamakin shi ne, mutumin nan fa shi ne ya dauki nauyin fim din kuma shi ne mai masaukin duk wanda ya je Zamfara aikin, to ya a ka yi bai san otel din da ta sauka ba har sai ya tambaye ta, alhali shi ne ma mai kama otel din bakidaya?

Da alamu dai tarihi ne kawai ya ke maimaita kansa, domin wannan lamarin ya tuno mi ni da wani al’amari na baya-bayan nan. A bayan afkuwar Badakalar Hiyana an kafa kwamitin da’a, domin hukunta wadanda ke zargi da aikata rashin da’a a cikin masana’antar Kannywood a karkashin jagorancin Ibrahim Mandawari.

Bayan kwamitin ya zauna sai ya yankewa wasu daga cikin masu sana’ar hukuncin dakatarwa, saboda zargin kama su da aikata halayya ta rashin da’a. Katsam sai daya daga cikin wadanda a ka yankewa hukuncin, wato Farida Jalal, ta fito ta gayawa mujallar Fim cewa, shugaban kwamitin ne ya kashe ma ta aure kuma shi ne ya nuna zalamarsa ta neman ta.

Wato abin nufi a nan shi ne, ‘macen bariki’ ta na da wani mugun makami da za ta iya cabawa duk wanda ya shiga gabanta, kuma Allah Ne kadai Zai iya fitar da shi daga zargi, amma ba dai tunanin dan adam. Watakila irin makami na ’yan bakiri ‘Malika’ ta aro ta cabawa Bazamfaren.

Wato da alamu lamarin ya na neman zama al’ada; duk yarinyar da a ka hukunta a Kannywood, to sai ta fito ta sheka wa wani ‘magana’. Ba a fi wata guda da dakatar da Maryam daga sana’ar shirin fim ba tsawon shekara biyu, saboda zargin aikata rashin da’a, sai ga shi ta fito ta daurawa daya daga cikin shugabanni a masana’antar jakar tsaba, kaji na neman bin sa. Shi dai Sani Zamfara ya na daya daga cikin jogogin shugabannin bangaren ’yan kasuwa, wadanda da wakilcinsu a ka yankewa Maryam wancan hukunci.

Hakika masana’antar shirin fim ta na fuskantar kalubale mai yawa. Akwai jarumai da yawa wadanda su ka jima su na neman a ba su dama, amma ba su samu ba. Lokaci guda Maryam ta shigo masana’antar a ka ba ta gagarumar gudunmawa, ba don ta fi kowa ba a ka sanya ta a manyan

finafinai, amma domin kawai nuna karamci ga ’yar uwarta, wacce ta rasu a yayin aurenta da dan uwa dan fim. To, amma sai ga shi Maryam ba ta gode ba, ba a kuma wanye da ita lafiya ba. Balaraba ta kasance har yau a na begen ta a masana’antar, domin an wanye da ita lafiya.

Watakila da Maryam ta sha wahala kafin ta sami daukaka a Kannywood, kamar yadda da yawa su ka sha wuya, watakila da ta mutunta karramawar da a ka yi ma ta, kuma wata kila da ba ta kalli alfarmar fim a matsayin wofi ba.

A karshe shawarar da zan ba wa Maryam ita ce, duk da dai ta shaidawa mujallar Fim fatanta na ganin ta samu makudan kudi a gidan mijinta fiye da yadda ta ke samu a sana’ar shirin fim, Ina mai tunatar da ita da cewa, aure ibada ne ba wajen neman kudi ba.

Idan Allah Ya sa aurenta Ya tsaya da kafarsa, to ta dauka cewa, ta je neman lada ne ba neman kudi ba. Hakan zai taimaka ma ta gaya a zamantakewarta da mijinta. Ina yi ma ta fatan alheri matuka! Bissalam!!!

http://hausa.leadership.ng/hausaleadreship9n.01.html