Babu Harshen Da Yake Mamaye Duniya Kamar Hausa —Helen Ward Al-Amin Ciroma — August 14, 2015
Na Ji Dadin Fitowa A Matsayin Sarauniya Badura Cikin ‘Magana Jari Ce’ Shekaru da dama bayan barinta kasar nan, AISHA HELEN WARD ta kasance daya daga cikin malaman dake koyar da harsunan Hausa da Turanci a kasar Landan. Malamar, har ila yau, daya ce daga cikin marubuta litattafan Hausa. Ba wannan kadai ba tauraruwar wasannin kwaikwayo ce. Wanda idan za a iya tunawa ita Sarauniya Badura a shirin ‘Magana Jari Ce’na Turanci shekarun baya.
A cikin wannan tattaunawar da ta yi da AL-AMIN CIROMA , Aisha Ward (Sarauniya Badura) ta yi tsokaci kan harkar rubutun adabin Hausa, kalubale da nasarori, kamar haka:
Da farko, ko za ki gabatar mana da kanki da dan takaitaccen tarihinki?
An haife ni kuma na tashi a Kaduna. Ni ce ‘ya ta biyu cikin ‘ya’yan mahaifina guda bakwai. Mahaifin namu ya yi aiki ne a kamfanin NITEL, kafin ya ritayar ajiye aiki na ganin damarsa a 1986. Mahaifiyata kuma mai kula da gida ce, ta kasance a gida tana aikin tabiyyar yara.
Alokacin, gidanmu gida ne na jami’a; farin ciki da jin dadi da juna. Babban gidan Kirista ne yawan maraba da kowa, inda ubamu ya karfafa neman ilimi da aiki da shi. Kullum ya kan gargade mu da fifita ilimi bisa komai. Ya kuma zama mana dole tun da uban namu shi malamin babban makarantan boko ne a da. Saboda haka, ya zama masa dole cewa duk ‘ya’yansa su yi karatu mai zurfi.
Batun makaranta kuwa, na halarci Kwalejin ‘yan mata ta Kawo mai suna St Faith’s Girls’ College Kawo, a cikin 1970. Bayan haka, ba da dadewa ba, na tafi Ingila a karshen 1980, inda na samu digirin farko, wato BA Honours, na kuma yin digiri na biyu, babban digiri (Masters) daga Jami’ar Kingston na Landan. A halin yanzu, ina bincike domin samun babban digiri na ‘PhD’ na Ilimi, ta hanyar Koyarwa Harshen Turanci.
HARSHEN HAUSATa yaya tsinci kanki a cikin harkar rubutun Hausa, kuma me ya fara ba ki sha’awa, ganin ba cikakkiyar Bahaushiya ba?
Akwai dalilai da yawa da ya sa na fara rubutu da Hausa. Na farko Hausa, harshe ne mai fa’ida, yana da cikakken bambancin kalmomi. Harshe ne na mai karin sauti; karin sautin kuma ya kan kara ma’anar kalmomi.
Duk ba ba cikakkiyar Bahaushiya ba, kamar yadda ka fada, amma ni Bahaushiyar Kaduna ce, na fara jin harshen Hausa tun ina tsummar goyo. Na tashi da harshen Hausa a bakina. Saboda ni ‘yar kasar Hausa ce, shi ya sa na yanke hukuncin fadawa cikin fagen adabin Hausa. Hakan kuwa ya zama mini dole lokacin da na fara koyarwar harshen Hausa ga dalibai a wata babbar cibiya a nan Ingila, ‘yan shekaru da suka wuce.
A wannan lokacin kuwa, sakamakon wani binciken da na yi, ya nuna cewa ana fama da tsananin rashin littattafan Hausa na koyarwa a kasuwa, ba ma nan cikin Ingila kawai ba, har ko’ina a duniya. kuma lokacin da na taimaka wa wata kafar sashen Hausa a wannan cibiyar, ya fuskanci suna tsananin bukatar littattafan karatu da na koyarwa kamar yadda sauran harshuna suke a Ingila, na kuma lura cewa hatta ‘yan kalilan da na tarar a cibiyar, wasu marubuta ne daga Yammaci suka yi. Babban abin damuwa ma shi ne littattafan sun tsufa sosai, domin wasu an rubuta su ne tun daga shekaru 80 – 90 da suka gabata.
Kuma tilas ne a ga bambanci tsakanin kalmomin da na yanzu. Har ila yau, na ga cewa yawacin ma’anar kalmomin da suke cikin wadancan littattafan, wadanda Yammanci suka rubuta, ba su yi daidai ba ne da yadda dan za a iya fahimtarsu a yau ba, musamman ga ‘yan kasar na wannan zamani.
Har ila yau, ‘yan’uwana malaman Hausa da dalibai suka yi kukan rashin isasshen kayan karatun Hausa a kasuwa, saboda haka, na yanke shawarar zan rubuta wani littafi domin amfanin dalibai da duk wadanda suke da ra’ayin koyon Hausar. Duk kuwa da sanin cewa littattafan Hausa ba su da kima sosai a idanun al’umma, musamman ma a kasuwa, amma ban karaya ba, na daure na wallafa littafin. Ka san akwai bambanci tsakanin rubutu domin dalibai kan Nahawu da kagaggun labarai.
Wani dalilin kuma da ya sa na ke rubutun Hausa shi ne karatun littafin Marigayi Alhaji (Dakta) Abubakar Imam, wato, ‘Magana Jari Ce,’ shekaru masu yawa da suka wuce. Ba kawai na karanta littafin ba, na kuma kasance daya daga cikin taurari cikin wasan kwaikwayon da aka yi kan littafin da harshen Turanci, ‘Wisdom Is An Asset,’ wanda aka rika nunawa a talbijin na kasa, NTA a shekarar 1980 zuwa 1989. Na fito a matsayin Sarauniya Badura (Kueen Badura).
Kafin ki fara tunanin yin rubutun Hausa, me ki ke yi?
Kafin na fara tunanin yin rubutu, bayan da na samu digiri na farko, na fara koyarwa a sakandare a nan London na ‘yan shekaru. Bayan da na samu digiri na biyu, na canza wuri zuwa jami’a da cibiyoyi mafi girma, duka a Ingila.
Mene ne sirrin samun nasarar kasancewa cikin harkar rubutunki?
Ai to, kamar yadda na bayyana a sama, an haife ni a Kaduna – dukanmu – ni da ‘yan’uwana, a nan aka haife mu muka yi girma da ilimi. Saboda haka, ba shakka ni Bahaushiyar Kaduna ce tare da cewa na fara ji da magana a harshen Hausa tun ina ‘yar kurciciyata. A gindanmu, babban harshen maganarmu shi ne Hausa. Kawai Allah ne ya hore mani wannan basirar, babu wani sirri. Ko da yake na dade da zama a Ingila, ai ba ya yiwuwa mutum ya manta da abin da aka haife shi a ciki.
Ya zuwa yanzu, litattafai nawa kika rubuta, kuma nawa aka fitar zuwa kasuwa, sannan wace hanya kike kasuwancinsu a can Ingila?
Na rubuta littattafai biyu ne kawai. Daya hadin gwiwa ne da wani marubuci; amma ‘Magana Sai Mai Ji’ ne wanda aka wallafa na farko wanda ni kadai na yi.
Batun kasuwanci kuma shi ne ta hanyoyin harkar intanet, wato ‘Amazon’ a Ingila, Amurka da sauran duniya, da kuma ta hanyan wuraren tallar littattafai na kwamfuta da yawancin dakunan karatu na duniya.
A halin yanzu, ina rubutun littattafai guda biyu na Turanci, sunayen su ‘The Many Names of God’ da ‘Sophie’s Birthday Surprise.’
Marubuta da yawa a nan Nijeriya suna da burin kasancewa a gaba-gaba wajen raya adabi. A fahimtarki, mene ne babban kalubalen da marubuta ke fama da su?
Harkar kalubale da ci gaban harkar rubutun Hausa a Nijeriya ya na dogon tarihi, tun daga lokacin shugabannin jihadi wadanda suka yi amfani da matsakaicin waka domin ilmanta da nemi goyon baya da kwarin gwiwar maibiyoyinsu. Tun daga lokacin, adabin Hausa ya daure ya fara fuskantar kalubale, musamman yadda suka Marigayi Abubakar Imam suka rika yi da zantukansu da sauransu. Amma a yau, duk da yake akwai fasahar zamani, akwai rashin marubutan adabin Hausa domin rashin ainihin ilimin na rubutun zunzurutun Hausar, da rashin sha’awar karatu, da kuma rashin tallafi daga gwamnanti. Dukkanin wadannan suna daga cikin matsalolin da marubuta ke fama da su.
Haka kuma, akwai wasu marubutan wasan kwaikwayo wanda aka sansu da sunan “Soyaya” wadanda matasa ne. Amma mafi akasarin jama’a ba su karbi ‘yan soyaya, kamar yadda ya kamata ba, saboda jama’a suna tsamani kaggagen littattafansu ba nagari ba. A gefe guda kuma littattafan ‘Soyayya’ sun kara tayar da kumajin matasa kan harkar rubuce-rubuce, sai dai manyan manazarta na kallonsu a matsayin na tsantsar al’adu ba ne, musamman wadanda ake yawan sanya harkar badala a ciki.
Duk da haka, marubuta litattafan ‘soyaya’ sun taimaka ainun wajen adana da tayar da ruhin adabin Hausa a Nijeriya ta yau.
Kafin barin ki Nijeriya, kina daya daga cikin wadanda suke fitowa a wasannin kwaikwayo a gidan talabijin. Masu karatu za su so jin yadda kika yi harkar a da?
E, lalle haka ne, kafin barina Nijeriya, ina daya cikin wadanda suke fitowa a wasannin kwaikwayo a gidan talabiji na Kaduna, kamar yadda na ambata a baya tun daga 1980 har zuwa 1990. Mun yi shirye-shirye da dama.
Na ji dadi wannan harkar kwarai da gaske. Na tuna a lokacin, wani lokaci, duk inda na shiga, mutane su kan ambaci sunana.
Zan iya tunawa da wasu daga cikin taurarin da muka yi shirin da su, Marigayi Isa Mayo (mijina a lokacin), Marigayi Magaji Ishak – Allaha’i jikansu, Ibrahim Buba, Ibrahim Abba Gana da sauransu. Wannan harkar ma ta kara min kumajin rubutu da Hausa.
Wasannin kwaikwayo a yau sun rikida sun zama manyan sana’o’i, shin yaya za ki kwatanta yadda aka fara da kuma abubuwan da ake yi a yanzu?
Haka ne, a shekarar 1960, babban shugaban BBC na harkokin Afirka ya gayyace marigayi John Stocbridge, ya shirya wani wasan kwaikwayo domin masu sauraro na Afirka, musamman a Nijeriya. John ya shirya, wasan kwaikwayon sabulu, wanda aka fara a Rediyon BBC a Landan. Daga baya aka fara wasan a Nijeriya da ko’ina a Afirka. Wasu cikin wasannin rediyo a lokacin sun hada da wata matar adabin Afirka, Ama Ita Aidoo da Saeed Jafrey. Tun daga lokacin ne wasannin kwaikwayo suka fara tasiri a cikin al’ummarmu. A lokacin babu talabijin, shi ya sa aka fara raja’a ga sauraren wasannin.
Amma halin yanzu, ga shi har sun zama manyan sana’oi da ci-gaba fasaha da ilimi. Sirrin nasarar yawancin marubuta da ‘yan wasan kwaikwayo shi ne yadda suka iya motsawa, suka iya baje kolin fasaharsu daga rediyo zuwa talabijin. A halin yanzu, wasannin kwaikwayo sun yi nisa, sun zama abin alfahari a kasuwannin duniya. Kuma na yi sha’awar yadda Nijeriya ta rika yi wa wasu sassan na duniya fintinkau.
Masana’antun wasan kwaikwayo da na fim sun samu ci gaba mara misaltuwa domin mutane ko a Nijeriya, mutane kamar su Ola Balogun, Kasimu Yero, Hubert Ogunde, Wale Soyinka, Marigayi Ken Saro Wiwa, Marigayi Adamu Halilu, Debra Ogazuma da sauransu, sun taka muhimmiyar rawa wajen habaka masana’antar. Babbar nasarar masana’antu fim na Nijeriya shi ne Nollywood, domin kuwa a wani bincike da aka yi a 2013, an ga cewa Nollywood ce kasa mafi daraja a masana’antu fim a duk duniya bayan samuwar kudaden shiga na triliyan 1.72 naira, wato kimamin dalar Amurka Milyan 10.
Ko za ki iya bayyana mana yadda aka yi har aka zabe ki don fitowa a matsayin Sarauniya Badura a shirin ‘Wisdom Is An Asset’ (Magana Jari Ce) na Dakta Abubakar Imam?
A lokacin da a ka fara tunannin yi wannan wasan a NTA Kaduna, Debrah Ogazuma, wanda ta shirya shirin, ta shiga neman ‘yan wasan kwaikwayo, maza da mata. Ta nema ta same su, ciki, har da Marigayi Isa Mayo. Amma daya kawai ba ta samu ba, ita ce wanda za ta fito a matsayin Sauraniya Badura.
To a lokacin, ita Debrah malamata ce lokacin da nike sakandare a Kawo Kaduna, wannan ta sa har ta gayyace ni, aka gwada ni, na kuma yi nasara. Nan take ta ba ni matsayin a wannan muhimmin shirin. Ka ji yadda aka zabe ni a matsayin Sauraniya Badura a shirin ‘Magana Jari Ce.’
Ba mu a takaice yadda kika fuskanci harkar wasan kwaikwayon da kika yi a Nijeriya.
Na ji dadin harkar wasannain kwaikwayo, musamman a shirin ‘Magana Jari Ce’ kwarai da gaske. Natuna a lokacin, wani lokaci, duk inda na shiga, mutane su kan nuna mani kauna, suna jin dadin irin rol din da nake fitowa a cikin shirin da sauransu. Aiki ne mai wuya domin rashin barci da dogon lokacin aiki, amma domin aiki ne wanda na ke sha’awa, ban kosa ba, na ji dadi sosai.
Shin har yanzu kina yin wasannin kwaikwayo a kasar Turai?
A’a, ba na yin wasannin kwaikwyo a nan Turai. A halin yanzu ni malama ce a jami’a.
Idan da masu shirin fim na Hausa a yanzu za su gayyace ki, za ki iya fitowa a finafinan Hausa da ake yi yanzu?
A halin yanzu aikin koyarwa sun yi mini yawa, amma idan aka gayyace ni, a lokacin da aiki ya ragu mini, ko kuwa a lokacin dogon hutuna, zan iya fitowa a finafinan Hausa, ko da fim daya ne. Wasan kwaikwayo ne soyyayata ta farko.
Shin kina kallon finafinan Hausa a yanzu?
E, na kan kalli finafinan lokaci lokaci. Suna da kyau kwarai da gaske. An kara kyautata harkar wasannin kwaikwayo a yau fiye da na da.
Daga karshe, wasu shawarwari za ki ba Marubuta da masu shirin finafinan Hausa a yau?
Shwarwarin da zan ba marubuta da masu shirin finafinan Hausa a yau shi ne su ci gaba da yi abin da suke yi, musamman su rika kyautata duk irin siddabarun da ake yi a fim domin ci gaba da raya adabin Hausa. Su kuwa marubuta su tabbatar cewa aikinsu ya ci gaba ta hanyar bunkasa harkar bincike da raya adabin Hausa. Kar mutum ya saduda da mafarki da kishin zucinsa.